Sanin Makamar Da’awa

 • An shirya wannan makala musamman saboda ‘yan uwa masu Da’awa na karamar Hukumar Dawakin Kudu da kewaye Mayu, 2015

بسم الله الرحمن الرحيم

Gabatarwa

Aikin Da’awa, watau kira zuwa ga addinin Allah da nasiha ga bayinsa, da umarni da kyakkyawan aiki da hani ga barin munkari, shi ne mafificin aiki da Musulmi zai shagala da shi. Dalili shi ne, Da’awa ita ce aikin Annbawa da Manzanni kuma ita ce tafarkin Annabinmu Muhammad (SAW) da dukkan Annabawan da suka gabace shi. Har yau, Da’awa ita ce tafarkin mabiyan Annabawa. Allah Maxaukaki yana cewa da Manzonsa (SAW), “Ka ce: Wannan ce hanyata, ina kira zuwa ga Allah a kan basira, ni da waxanda suka bi ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Ni kuma ban zama daga masu shirki ba.” (Suratu Yusuf: 108).
Har yau, Allah ya umarci Annabi (SAW) da yin da’awa. Ya ce, “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau.” (Suratun Nahal: 125).
Saboda haka, babu wani aiki mai daraja da xaukaka kamar wa’azi da koyarwa da yin nasiha ga bayin Allah. Sai dai, kafin mutum ya shiga wannan aiki mai alfarma da fa’ida, yana bukatar shiryawa da horo da qwarewa. Watau kamar yadda ko wane aiki ba’a shigar sa sai bayan an san makamarsa, to haka shi ma mai Da’awa yana bukatar sanin makamar Da’awa. Kuma wannan shi ne maulu’in wannan taqaitacciyar maqala.

Sanin Makamar Da’awa

Kafin mutun ya shiga aikin Da’awa, akwai ilmai da fannoni da ya kamata ya karanta su kuma ya qware a kansu dai-dai gwargwado. Waxan nan sun haxa da:

1. Alqur’ani mai girama. Ya kamata mai Da’awa ya karanta Alqur’ani, ya haddace shi duka, ko kuma ya haddace abinda Allah ya hore masa dai-dai iyawarsa. Haka nan, yana bukatar Tajwidinsa da kyautata karatunsa da lazimtar tilawarsa safe da yammaci. Lallai ne Alqur’ani mai girma ya zama tare da shi a ko wane lokaci.

2. Sunna ko kuma Hadisan Annabi (SAW). Ana bukatar mai aikin Da’awa ya Sunnar Annabi (SAW), ya kiyaye da Hadisansa kuma ya san ilmin Ruwaya da Diraya, watau ilmin ruwayar Hadisan da kuma ilmin bambance tsakanin Hadisi ingatacce da Hadisi mai rauni. Kuma ya kamata ya san littafan Hadisi dai-dai gwargwado.

3. Fiqihu. Mai Da’awa yana bukatar ya san ilmin Fiqihu, ya kiyaye da mas’alolin ibada da ma’amala. Kuma babu laifi ya zama banda Mazhabarsa, ya yi tsinkaye a kan wasu Mazhabobin da irin savanin dake tsakanin malamai. Wannan zai taimaka masa a wajen ba da fatawa.

4. Tarihi. Ilmin Tarihi yana da muhimmanci ainun ga mai Da’awa. Lallai ne ya karanta Sirar Annabi (SAW), watau tarihin rayuwarsa mai tsarki, da rayuwar Sahabbansa Yardaddun Allah, da irin Jihadi da gwagwarmaya da sadaukar da kai da suka yi wajen yaxa Addinin Allah. Kuma har yau, mai Da’awa ya san:

 • Tarihin Daulolin Musulunci.
 • Rayuwar Gwarzayen Musulunci tun daga Sahabbai.
 • Tarihin Harakokin Musulunci da jagororinsu.
 • Tarihin al’ummai, musamman wadanda muke da alaka da su.

5. Ilimin Luga. Wajibi ne, wajabci mai karfi, a kan mai Da’awa ya san Lugar Larabci, saboda Qur’ani da Hadisi ba su fahimtuwa idan babu Ilmin Larabci.
6. Ilmin Yau. Wannan fanni yana da matuqar muhimmanci ga mai Da’awa, domin Da’awa a yau sai xan yau! Ilmin Yau, wanda malamai suke kira Fiqihul Waqi’i, yana nufin mutun ya waye, ya zama yana faxake da yanayin rayuwa na zamaninsa, da al’amuran siyasa da tattalin arziki da zamantakewa, ba na Musulmi ko na qasarsa kawai ba, a’a har da na sauran al’umman duniya baki xaya. A wajen tabbatar da wannan ilmi ana bukatar sanin fannoni da al’amura kamar haka:

 • Ilmin Jogurafiyya, watau inda qasashe suke da maqotansu
 • Tsarin siyasa ta qasarsa da sauran qasashe
 • Tattalin arziki na qasarsa da sauran qasashe
 • Sanin yanayin rayuwar qasarsa, musamman idan yana zaune da wadanda ba Musulmi ba akasar
 • Sanin yanayin rayuwar Musulmi a kasashe daban-daban

Halayen Mai Da’awa

Babu shakka kyawawan halaye su ne ruhin Musulunci. Wannan ya sa Manzo (SAW) yake fadi a cikin hadisi ingantacce, “An aiko ni ne kawai domin in cikashe kyawawan halaye.” A wani hadisin kuma ya ce, “Mafifitanku kusanci da ni a Ranar Alqiyama su ne mafiyanku kyawawan halaye.” Don haka mai Da’awa, a matsayinsa na mai bin tafarkin Annabi kuma mai koyi da shi, dole ne ya sifantu da kyawawan halaye waxanda za su taimaka masa wajen cin nasara a aikinsa na Da’awa. Daga cikin irin wadannan halaye akwai:

1. Haquri da yaqini. Mai Da’awa yana bukatar haquri da sakankancewa da taimakon Ubangiji saboda tafarkin Da’awa yana da tsawo, don haka sai mai haquri ne zai kai gaci. Har yau, haquri da yaqini su ke kai mutum ga matsayin shugabanci a addini. Allah Maxaukaki ya ce, “Kuma mun sanya shugabanni daga cikinsu, suna shiryarwa da umarninmu, a lokacin da suka yi haquri, kuma sun kasance suna yin yaqini da ayoyinmu.” (Suratus Sajada: 24).

2. Tsoron Allah a cikin magana da aiki.

3. Sauqaqawa da yassarewa. Manzon Allah (SAW) ya ce, “An aiko ni da tafarki miqaqqe, mai sauqi.” Kuma ya ce, “Ku sauqaqa, kada ku tsananta. Ku yi albishir, kada ku kore mutane.” Har yau, ya ce: “Lallai ku an aiko ku kuna masu sauqaqawa, ba masu tsanantawa ba.”

4. Dakewa da juriya.

5. Dogaro da kai. Lallai mai Da’awa ya dogara da kansa a wajen abincinsa da bukatun rayuwarsa, kada ya zura ido ga abin hannun mutane. Don haka, dole ya zama mai sana’a ko kasuwanci da zai riqa cin halali da shi.

6. Wadatar zuci da gudun duniya. Mai Da’awa ba ya sa rai da sakamakon duniya, don haka ba ya damuwa da tara abin duniya, ko samun xaukakar duniya.

7. Tawalu’u da fifita mutane. Da waxan nan sifofi ne zai jawo mutane zuwa gare shi, kuma su saurari abinda yake faxi, su yi aiki da shi.

8. Nuna kyakkyawan misali. Wannan yana tabbata da abubuwa biyu:

 • Yin Da’awa da aiki kafin magana.
 • Ya aikata abinda yake kiran mutane zuwa gare shi.

Dangane da wannan, Allah Madaukaki yana jan kunnen Muminai. Ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani! Don me kuke faxin abinda ba ku aikatawa.” (Suratus Saff: 2). A dangane da batu a kan Ahalul Kitabi, Allah Maxaukaki ya ce, “Shin, kuna umarnin mutane da alheri, kuma ku manta da kanku alhali kuwa kuna karatun Littafi? Shin, ba za ku hankalta ba?” (Suratul Baqara: 44).

Zabar Fagen Da’awa

Akwai fagage da dama da salo dabam-daban na Da’awa da mutum zai xauka gwargwadon iyawarsa da yanayin qasarsa da bukatun zamaninsa. Tana yiwuwa mutun ya haxa fage biyu, ko salo sama da xaya, gwargwadon bukata da iyawa.
Salo-Salo na Da’awa:

 • Magana ta fatar baki, ko wa’azi
 • Darasu ko koyar da littafai a gida ko a masallaci
 • Rubutu na littafai, musamman qanana, ko qasidu
 • Rubutu a jaridu da mujallu
 • Magana, wa’azi ko darasi a radiyo da talabijin da sauran su

Fagagen Da’awa:

 • Tunasar da Musulmi
 • Kiran Kiristoci zuwa Musulunci
 • Kiran Maguzawa zuwa Musulunci
 • Yakar Bidi’o’i da ‘yan Bidi’a

Wanne Yafi Muhimmanci?

Koda yake muna da nau’i biyu na waxanda ba Musulmi ba a qasarmu, ina nufin Kiristoci da Mushirikai ko Maguzawa, amma duk da haka yaqar bidi’a da ‘yan bidi’a ya fi muhimmanci a kan kiran waxan nan kafiran zuwa Musulunci. Wannan shi ne ra’ayin magabata daga malaman Sunna.

Yaqar Bidi’a Ya Fi Ibadar Nafila

An tambayi Imam Ahmad binu Hanbal, Allah ya rahamshe shi dangane da mutane biyu: xaya yana azumi, yana salla, yana i’itikafi, xayan kuma yana gargaxi a kan ‘yan bidi’a. Wa ya fi? Sai ya ce, “Idan mutum ya yi tsayuwar dare, ya yi sallah, ya yi i’itikafi, wannan kansa yake yiwa. Amma idan ya yi gargaxi a kan ‘yan bidi’a, to wannan Musulmi yake amfana. Don haka ya fi.”

Yakar Bidi’a Yafi Jihadin Kafirai

Babban malamin Sunna, Yahya binu Yahya, ya ce, “Kare Sunna ya fi jihadi.” Sai aka tambaye shi: Mutum ya kashe dukiyarsa, ya yi fama da kansa, ya yi jihadi, amma mai kare Sunna ya fi shi? Sai ya ce, “E, ninkin ba ninki!”

Bidi’a Mafi Muni

Kuma koda yake muna da nau’in bidi’o’i da dama a qasar nan, amma mafi sharri, mafi muni, kuma mafi kaushi ita ce bidi’ar SHI’A. Domin wannan mummunar bidi’a ta tattare miyagun aqidoji masu warware imani, kuma ga haxari ga rayuwar duniya.

Miyagun Akidun Shi’a

 • ‘Yan Shi’a suna kafirta Sahabban Annabi (SAW) baki dayansu, in banda guda bakwai kawai.
 • ‘Yan Shi’a suna zagin Sahabbai, suna yi musu qazafi, suna ci musu mutunci, haka nan suna zagin Uwayen Muminai matan Manzon Allah (SAW) kuma suna yi musu qazafi.
 • ‘Yan Shi’a ba su yarda da khalifancin Khulafa’ur Rashiduna ba, watau Abubakar da Umar da Usmanu, Allah ya qara musu yarda, sai Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara masa yarda, shi kaxai suka yarda da khalifancinsa.
 • ‘Yan Shi’a suna quduri da khalifanci (ko imamancin) Imamai goma sha biyu: Ali, Hassan, Hussaini, Ali Zainul Abidin, Muhammad Baqir, Ja’afar Sadiq, Musa Kazim, Ali Rida, Muhammad Taqiy, Ali Naqiy, Hassan Askari da na sha biyunsu Mahadi wanda suka ce wai an haife shi tun shekaru dubu da xari biyu da suka wuce, amma ya vuya yana xan shekara huxu, kuma zai bayyana a qarshen zamani ya kafa daular Shi’awa wacce za ta ga bayan Ahalus Sunna.
 • ‘Yan Shi’a suna quduri da cewa waxan nan Imamai goma sha biyu sun fi dukkan Annabawa da Manzanni da Mala’iku makusanta ga Ubangiji.
 • ‘Yan Shi’a suna quduri da cewa Imaman sun san gaibu, sun san abinda ya faru tun farkon halitta da abinda zai faru har bayan abada, kuma sun san abinda yake qunshe cikin zukatan bayi.
 • ‘Yan Shi’a suna imani da cewa Alqu’ani da yake hannun al’umma a yau, wanda kuma Musulmi ke tilawarsa a safe da yammaci, ba dai-dai yake ba, an yi qari da ragi a cikinsa, kuma wai Sahabbai ne suka yi wannan qari da ragin.
 • ‘Yan Shi’a suna imani da cewa Karbala ta fi Makka da Madina falala, kuma wai ita ce alqiblar Musulmi ta haqiqa!
 • ‘Yan Shi’a sun yarda da Auren Mutu’a kuma suna yin sa, haka nan suna saduwa da matansu ta baya.
 • Wadannan kaxan ne daga cikin miyagun aqidojin ‘yan Shi’a masu raba Musulmi da imaninsa. Don qarin bayani, duba littafin Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a da Akidojinsu.

Hadarin Shi’a ga Duniyar Musulmi

Kamar yadda Shi’a take hadari ga addinin Musulmi da akidunsu, haka kuma hadari ce ga rayuwarsu ta duniya, domin tana kawo rashin zaman lafiya da zubar da jinni. Ga misali kadan daga wasu kasashe:

 • Lebanon: Wannan kasa ita ce mazaunin kungiyar Hizbullah, kungiyar ta’addanci mafi karfi a Gabas ta Tsakiya, wacce ‘yan Shi’a na kasar Iran suke amfani da ita a wajen ayyukansu na ta’addanci a kasashen Musulmi.
 • Siriya ko Sham: Kasar Iran tana taimakon gwamnatin Bashar Asad ta tsuraru ‘yan Shi’a wacce take kafsa yaki da ‘yan tawaye masu bin tafarkin Sunna, wadanda kuma su ne mafiya rinjaye, tun farkon shekarar 2011. Gwamnatin Asad ta dogara kacokan da taimakon Iran, na kudade da makamai da kwararrun sojoji, wajen ta’addancinta a kan ‘yan kasarta Ahalus Sunna. ‘Yan Shi’ar Siriya sun rushe kimanin kashi biyu bisa uku na dukkan biranen kasar na Ahalus Sunna, sun kashe sama da mutane dubu dari biyu da hamsin (250,000), sun kore sama da mutane miliyan shida (6,000,000) daga gidajensu. Banda wannan kuma, ‘yan Shi’ar Siriya suna amfani da muggan makamai wadanda aka haramta a dokokin kasa da kasa wajen aikata kisan kare-dangi a kan Ahalus Sunna.
 • Yaman: Kasar Iran tana ba da taimakon makamai da kudade da kwararrun soji ga ‘yan tawayen Hutsawa marasa rinjaye, masu bin tafarkin Shi’a, a kokarinsu na danne Ahalus Sunna da mulkar su da karfin tuwo.
 • Iraqi: A Iraqi kuwa, kasar ‘yan Shi’a ta Iran ta taimakawa ‘yan Shi’ar wannan kasa wajen kafa kungiyoyin ina-da-kisa wadanda suke karkashe Musulmi mabiya Sunna, suna rushe biranensu, suna kore su daga gidajensu.
 • Nijeriya: ‘Yan Shi’ar Nijeriya mabiyan Zakzaki suna yin mugun tattali na farma Ahalus Sunna tare da taimakon kasar Iran. A cikin watan Oktoba, 2010, jami’an tsaro sun kama kontena goma sha uku maqare da miyagun makamai a tashar jiragen ruwa ta birnin Legas. Bincike ya tabbatar da cewa wadannan makamai sun fito ne daga kasar Iran, kuma an aiko da su zuwa ga ‘yan Shi’ar Nijeriya mabiyan Zakzaki. Ofishin jakadancin kasar Iran a Abuja ya amsa cewa daya daga cikin mutanen da aka kama da makaman ma’aikacinsu ne. Bayan shari’a da ta dauki sama da shekaru biyu, an samu mutane biyu da laifi, ciki har da jami’in jakadancin na Iran, kuma kotu ta daure su shekaru 17 kowannensu.
 • A cikin watan Fabrairu, 2013, jami’an leken asiri na Nijeriya sun cafke wasu samari da suka yi karatu a kasar Iran, suna shirin kai hare-haren ta’addanci da nufin kashe wasu shugabannin Musulmi na kasarnan, ciki har da tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida, da Sarkin Musulmi mai murabus, Sultan Ibrahim Dasuki. Bayan bincike, an tabbatar da cewa wadannan samari suna yi wa kungiyar ta’addanci da Iran ke mara wa baya, watau Hizbullah, aiki ne. Jaridun kasarnan da kafafen yada labarai na kasashen ketare duka sun ruwaito wannan labari.
 • Hakanan, a wannan shekara dai ta 2013, an gano makamai masu yawa boye a wani gida a birnin Kano. Bayan bincike, an zargi wasu Kwarori ‘yan kasar Lebanon, wadanda ake jin suna da alaka da kungiyar ‘yan Shi’a ta Hizbullah, da mallakar wadannan makaman. Har yanzu maganar tana gaban kotu.
 • Wannan kungiya ta Hizbullah, ko kuma Hizbush Shaidan, wacce take adana makamai a Kano saboda mugun nufi ga Musulmin Nijeriya, ‘yan Shi’ar kasarnan karqashin jagorancin Ibrahim Zakzaki suna daga tutar ta a fili a wajen jerin gwano da suke gudanarwa a birane da yankunanmu na karkara.

Rufewa
Daga abinda ya gabata, muhimmancin Da’awa zai bayyana a fili ga dukkan mai tunani. Babu shakka, al’ummar Musulmi suna bukatar Da’awa fiye da yadda suke bukatar abinci da magani. Abinci yana gusar da yunwa ne ya gina jiki, magani yana gusar da cuta ya inganta jiki, Da’awa kuwa tana gusar da jahilci ta gina zuciya ta inganta ruhi. Magani da abinci amfaninsu kai tsaye na duniya ne; Da’awa kuwa amfaninta na duniya ne da lahira.
Gwamnatocinmu a yau suna kula da abinci da magani, amma ba ruwansu da Da’awa. Suna da Ma’aikatar Gona da Ministanta, da Ma’aikatar Lafiya da Ministanta, kuma suna ware musu kudade na musamman a kasafin kudi na shekara-shekara. Da’awa kuwa sai sadaka da karo-karo. Da gwamnatocinmu sun sani da sun ba Da’awa muhimmancin da ya dace da ita. Amma ba su sani ba!!
Don haka ya rage ga al’umma a kowanne birni da kauye, a ko wace jiha da karamar hukuma, su tashi tsaye da al’amarin Da’awa. Matasan Karamar Hukumar Dawakin Kudu sun yi nasu kokari. Allah ya saka musu da alheri.

Saura ina naku?