Gudunmawar ‘Yan Agaji ga Zaman Lafiyar Kasa

Jawabin Babban BaKo a Bikin Rufe Taron Bita ga ‘Yan Agaji na Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) da aka gabatar a garin Dutse, Jihar Jigawa, daga Laraba 12 zuwa Lahadi 16 ga watan Yuni, 2013
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi babu mai vatar da shi, kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su tabbata a gare shi da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.

Gabatarwa: Tubalan Ginin Izala
An xora ginin Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah a kan shika-shikai uku. Na farko Majalisar Malamai. Wannan ita ce zuciyar Qungiya da qwaqwalwarta wacce daga nan take samun koyarwa da fuskantarwa da haskakawa.
Na biyu Shugabanci na qasa mai ikon zartaswa. Wannan shi ne hannun daman Qungiya dake xauke da nauyin gudanarwa da aiwatar da manufofin qungiya a qasa.
Na uku sashen Agaji wanda ya qunshi dakarun Qungiya masu taimakawa sauran shika-shikan biyu wajen cimma manufofin qungiya da tsare ayyukanta na yau da kullum. Kuma wannan shi ne maudu’in maqalarmu a yau.

Falsafar Izala da Manufofinta
Falsafar JIBWIS da aqidojinta da manyan manufofinta a bayyane suke tun daga sunanta. Jama’a ce wacce ta kafu domin raya Sunnah da rushe bidi’a. Alqur’ani da Hadisi su ne mavuvvugar tunaninta kuna jagoran ayyukanta. Manufarta ita ce haxa kan al’umma a kan gaskiya, da zaburar da Musulmi domin su yi hidima ga addininsu da al’ummarsu, da kuma tabbatar da zaman lafiya da lumana a tsakanin dukkan ‘yan qasa.
Wannan jigo da waxannan manufofi a kansu ne aka kafa vangaren Agaji na qungiyar, kuma a kan haka yake gudanar da ayyukansa.

Samari Masu Jini a Jika
Kafin in yi nisa a cikin maqalar, bari in bayyanawa jama’a cewa yawancin ‘yan Agajin JIBWIS samari ne masu jinni a jika, kuma qungiyar tana ba su tarbiyyar Musulunci ga samari. (Idan ka xabe Darektan nasu, Engr. Mustapha Imam Sitti, wanda ko shi ba ragon tsoho ba ne, irin tsohon da ake cewa mai daka wa yaro kashi ne!) Musulunci yana yiwa samari tarbiyya ta imani da aikin qwarai, sai su zama yara a shekaru amma manya a ayyuka da tunani. Kuma irin wannan tarbiyya ce JIBWIS take baiwa ‘yan Agajinta.

Alqur’ani ya ba mu labarin irin waxannan samari a cikin Suratul Kahafi. Allah maxaukaki ya ce:

“نحن نقص عليك نبأهم بالحق، إنهم فتية آمنوا بربهم وزدناهم هدى. وربطنا على قلوبهم إذ قاموا فقالوا ربنا رب السماوات والأرض لن ندعوا من دونه إلها لقد قلنا إذا شططاب” (الكهف: 13-14)

Ba kawai bayin Allah zavavvu ba, yawancin annabawa ma samari ne. Mu duba labarin Annabi Ibrahimu lokacin da yake gwagwarmaya da mushirikai na mutanensa. Ya ce:

“وتالله لأكيدن أصنامكم بعد أن تولوا مدبرين. فجعلهم جذاذا إلا كبيرا لهم لعلهم إليه يرجعون. قالوا من فعل هذا بآلهتنا إنه لمن الظالمين. قالوا سمعنا فتى يذكر هم يقال له إبراهيم.” (الأنبياء: 57-60)

Annabi Isa (AS) shi ma saurayi ne. Ya fara da’awa yana xan shekara 30 kuma Allah ya xauke shi zuwa sama yana da shekaru 33.
Har Annabinmu Muhammad (SAW) shi ma ba tsoho ba ne. Ya fara da’awa yana da shekaru 40. Haka nan manyan Sahabbansa duka samari ne, domin yawanci ya grime musu da shekaru. Ya girmi Abubakar da shekara uku, Umar da kimanin 15, Usmanu da kimanin ishirin da wani abu.

JIBWIS tana koyi da magabata wajen tarbiyyar ‘yan Agajinta waxanda yawancinsu matasa ne. Tana ba su ladubba waxanda suke mayar da su yara a shekaru amma manya a tunani da ayyuka.

Ladubban ‘Yan Agaji
‘Yan Agaji a matsayinsu na masu sa rigar Sarki (watau uniform) suna samun horo da koyarwa na musamman daga Qungiya. Waxannan horo da koyarwa suna baiwa ‘yan Agajin wasu ladubba waxanda suke rabe su da sauran mutane da sauran qungiyoyi dabam-daban masu sa kayan Sarki. Kuma ladubban dukkaninsu ladubba ne na Musulunci waxanda aka tsamo su daga Alqur’ani da Sunnar Annabi (SAW).

Kyautata Niyya
Abu na farko da ake xora xan Agajin Izala a kansa shi ne kyautata niyya da yi domin Allah. Kasancewar ayyukan JIBWIS duka ayyuka ne na addini kuma na sa kai (watau ba na biya ba), wannan ya sa niyya a cikin aikin qungiyar take da muhammanci ainun. Kuma wannan ya yi dai-dai da koyarwar Annabi (SAW) inda yake cewa:
“إنما الأعمال بالنيات وإنما لكل امريء ما نوى.”

Saboda xan Agajin Izala ba ya jiran biya ko yabo daga wajen wani, sai dai ladan Allah kawai, wannan ya sa yana yin aikinsa da matuqar kyautatawa a koina ya samu kansa, kuma a ko wane hali. Haka nan, wannan ya sa babu cin dunduniya ko hassada a cikin aikin, sai ‘yan uwantaka da taimakon juna. Yana da wuya mutum ya samu wasu masu aiki tare da suke da haxin kai da son juna irin na ‘yan Agajin Izala.

Biyayya ga Shugabanni
Aikin sa rigar Sarki (ko kuma mu ce aikin xamara) ya gaji biyayya da amsa umarni, amma biyayyar ‘yan Agajin Izala ga shugabanninsu da sauran shugabannin Qungiya ya kai matakin buga misali. Kwamandoji da jami’ai da kurata duka suna bin umarnin na gaba da su, cikin ladabi da fahimta da ban girma. Babu shakka wannan ba zai rasa nasaba ba da tarbiyyar Alqur’ani da JIBWIS take yi wa ‘ya’yanta da mabiyanta da kuma musamman ‘yan Agajinta. Allah mai girma da xaukaka yana cewa:

“يأيها الذين آمنوا أطيعوا الله وأطيعوا الرسول وأولي الأمر منكم” (النساء: 59)

Aiki da wannan aya, da wasu ayoyi masu kama da ita, shi ya sa ‘yan Agajin JIBWIS suka yi fice wajen xa’a da biyayya, kuma shi ya sa suke yin aikinsu cikin lalama da lumana da nasara duk da gauraya da mutane masu yawa, masu mabanbantan halaye.

Haquri da Kamun Kai
‘Yan Agajin JIBWIS sun yi fice da tsananin haquri da riqon ragamar kai (watau ضبط النفس) ta yadda ba za ka tava samun xan Agaji yana sa-in-sa da wani mutum ba a bakin aikinsa. Maimakon haka, suna jure halayyar mutane, su tausasa musu, su bi su sannu har su kai su ga abinda suke bukata na dimantar tsari da bin doka da kaucewa duk abinda zai cutar, musamman a cikin taruka da gwamutsin mutane. Idan mutum ya duba, sai ya ga ‘yan Agaji a wajen ma’amalarsu da mutane a kan aikinsu, kamar suna tuna faxin Allah:

“وجعلنا بعضكم لبعض فتنة أتصبون” (الفرقان: 20)

Watau kai ka ce jarraba su ake yi. Ana qara matsa lamba, suna qara haquri!

Kau da Kai ga Barin Yasaccen Zance
Wani abu da ‘yan Agajin Izala suka shahara da shi, kuma suka sha bam-ban da saura, suka tsere sa’a, shi ne kau da kai ga barin duk abinda zai shagaltar da su ga barin aikinsu. Wanda ba’a shiga gonarsa ba ya yi haquri ba shi ne mai haquri ba, amma wanda aka ja shi, aka tone shi, aka shiga sabgarsa kuma ya qyale, shi ne haqiqanin mai haquri. ‘Yan Agaji ba sa bari a ja su zuwa ga jidali ko abinda bai kamata ba. Idan aka faxa musu mummunar magana ba sa mayarwa. Sai suka dace da sifar Muminai, kamar yadda Allah ya ba da labarinsu:

“والذين هم عن اللغو معرضون.” (المؤمنون:3)

Ko kuma a wa ayoyin inda yake sifanta su:

“وعباد الرحمن الذين يمشون على الأرض هونا، وإذا خاطبهم الجاهلون قالوا سلاما.” (الفرقان: 63)

‘Yan Agaji aikinsu suka sa a gaba. Idan gari aka je wa’azi suke wucewa gaba, su share fage. Idan Hajji aka tafi su ne ‘yan xaukar kaya, da nusarwa. Rani da damina, sanyi da zafi, dare da rana: waxannan duka ba sa damun ‘yan Agaji. Aikinsu suke yi ba sauna! Kirarinsu faxin Allah maxaukaki:

“وقل اعملوا فسيرى الله عملكم ورسوله والمؤمنون” (التوبة: 105)

Akwai wata magana da marigayi Sheikh Ja’afar ya yi (Allah ya jiqan sa). Ya ce shi yana ganin a Lahira sai ‘yan Agaji sun shiga aljanna kafin malamai masu wa’azi su shiga. Ya ce saboda su ‘yan Agaji aikinsu suke yi ba riya, ba nifaqa, su kuwa malamai masu wa’azi wata qila wasu akwai riya, ko hassada a cikin aikinsu. Ya ce su ‘yan Agaji abinda ya dame su shi ne a yi wa’azi a gama lafiya. Sheikh Abdulwahhab Imamu Ahalis Sunnah wal Jama’a ne ya hakaito wannan maganar a gaban Sheikh Yakubu Musa Sautus Sunnah. Wannan magana daga Sheikh Ja’afar, wanda ya kwashe shekaru aru-aru yana aikin da’awa a cikin qungiyar Izala, tun yana xan rakiya mai xaukar takalma har ya zamo daga cikin manyan malaman Izala, shaida ce babba ga ‘yan Agajin JIBWIS.

Ayyukn ‘Yan Agaji
‘Yan Agajin JIBWIS suna gabatar da muhimman ayyuka waxanda suke buqatar haquri da juriya da ladabi. Ayyukan sun haxa da kula da zurga-zurgar jama’a a wuraren taruka da nuna hanya da tsare doka da oda. Taimakon alhazai a nan gida da kuma a qasa mai tsarki, yana cikin ayyukansu. Har yau, suna gabatar da ayyukan agaji da taimakon farko yayin bukata a ko wane lungu da saqo na qasar nan, har da qasashen waje. A wajen waxannan ayyuka duka, ‘yan Agajin JIBWIS suna qarfafa aikin Gwamnati na tsaron rayukan ‘yan qasa da dukiyoyinsu, ta hanyar taimakawa ma’aikatan hukuma masu sanye da kayan Sarki, da ba su cikakken haxin kai. Kuma babu shakka, wannan babbar gudunmawa ce ga zaman lafiyar qasa da tabbatar da bin doka da oda a tsakanin al’umma.

Shawarwari
A qarshen wannan xan taqaitaccen bayani, ina ganin ya kamata in gabatar da wasu shawarwari waxanda nake ganin za su inganta aikin ‘yan Agajinmu, in Allah ya yarda. Shawarwarin na kasa su gida-gida kamar haka:

Sadarwa: Babu shakka ‘yan Agajinmu suna da kyakkyawan tsarin sadarwa, sai dai tsarin yana bukatar a inganta shi kuma a zamanantar da shi. Haka nan, tanadin qarin kayan sadarwa na zamani zai taimaka ainun wajen bunqasa ayyukan ‘yan Agaji, musamman duba da yadda wannan Qungiya mai albarka take ta samun buxi da qaruwar mabiya a wannan zamani.

Horaswa: ‘Yan Agajinmu suna samun horaswa mai inganci, kuma tarbiyyar Musulunci tana qara inganta aikinsu a fage. Sai dai qalubalen yau yana tilasta qara lura da horaswa da kuma sabunta salon horon da ake ba su, yadda za su iya tunkarar duk wani yanayi da ka taso wanda zai buqaci aikinsu. Saboda haka, qari a kan agajin farko, ‘yan Agajinmu suna bukatar sanin dabarun fitar da mutanen da wata musiba ta rutsa da su daga cikin dogayen gine-gine, ko ababan hawa, kamar jiragen sama, misali.

Kayan Aiki: Lallai Qungiya tana kulawa da ‘yan Agaji wajen samar masu da kayan aiki don inganta ayyukansu, amma bunqasar Qungiyar da qaruwar mabiyanta suna wajabta ninka himma wajen samarwa da ‘yan Agaji kayan aiki na zamani. Ga misali, a wajen sufuri ‘yan Agajin JIBWIS suna da motoci masu lafiya, amma a yau suna bukatar manyan babura domin kutsawa wurin da mota ba ta iya shiga, kuma domin yin rakiya ga malamai da shugabannin Qungiya.

A qarshe, ina roqon Allah maxaukaki da ya taimaki wannan qungiya, ya tsare ta, ya qara wa shugabanninta basira, himma da hangen nesa. Shugabanninmu na addini da na siyasa, muna roqon Allah ya qarfafi guiwarsu, ya taya su sauke amana da ya aza musu. Mu kuma mabiya Allah ya ba mu haquri da juriyar biyayya da fatan alheri. Allahumma amin.

Wassalamu Alaikun wa Rahamatullah wa barakatuhu.