Bayanin Bako Mai Jawabi

Bayanin Bako Mai Jawabi a Taron Bikin Kaddamar da Littafin Tafarkin Sunnah
na Ibnu Taimiya Laraba 22 Afrilu, 2009 Sakkwato

Gabatarwa

Da Sunan Allah Mai Rahama, Mai jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah Maxaukaki wanda ya haxa mu a wannan taro domin qaddamar da littafin Tafarkin Sunnah na Bijimin Malami, Gagara-Badan malamai, Shaihun Islami Abul Abbasi Ahmad binu Abdul-Halim binu Abdus Salam binu Taimiya – Allah Ya rahamshe shi. Babu shakka wannan littafi ya ci sunansa, Tafarkin Sunnah, saboda abinda ya tattare na tushen addini da gangariyar koyarwa to Sunnah a bisa tafarkin magabata na gargaru. Wannan littafi ya qunshi tattaunawa ta ruwan sanyi, kamar yadda masu fassara suka yi masa take, tsakanin Ibnu Taimiya da, ba ‘yan Shi’a kawai ba, amma da ‘yan bidi’a baki xaya. Littafin wata babbar taska ce wacce ta tattare gwala-gwalai na kayan gadon annabta, watau hadisan Annabi (SAW) da maganganun Sahabbansa da ijtihadin Tabi’ai da ra’ayoyan limaman mazhabobi hudu, da wasunsu. An yiwa littafin kawa da ayoyin Alkur’ani, an yi masa kwalliya da hadisan Annabi (SAW) ingatattu; kuma an cikashe qawarsa da kwalliyarsa da maganganun malamai magabata na gari. Don haka sai littafin ya zama gagara-gasa a fanninsa, ya zama wani rumbu na ilmi wanda ba’a iya wadatuwa ga barinsa a fagen yaxa Sunnah da yaqar bidi’a. Babu shakka fassara wannan littafi da yaxa shi tsakanin jama’a wani babban ci gaba ne a yunqurin sake jaddada Tafarkin Sunnah a wannan qasa
Tafarkin Sunnah da muke kira zuwa gare shi

Wata kila zai yi kyau a yi amfani da wannan dama, ta kaddamar da wannan babban littafi, a yiwa jama’a bayani, koda a takaice, na tafarkin Sunnah da muke kira zuwa gare shi Wane ne wannan tafarkin da muke kira zuwa gare shi? Tafarkin Sunnah da muke kira gare shi shi ne Tafarkin annabawa, shi ne “milkata Ibrahim”. Allah Madaukaki Yana fadi dangane da wannan tafarki:

ثم أوحينا اليك أن اتبع ملة ابراهيم حنيفا وما كان من المشركين (النحل: 123 )

Kuma Yana cewa:
ومن أحسن دينا ممن أسلم وجهه لله وهو محسن واتبع ملة ابراهيم حنيفا، واتخذ الله ابراهيم خليلا (النساء : 125 )

Kuma har yau Yana cewa:
قل انني هداني ربي الى صراط مستقيم دينا قيما ملة ابراهيم حنيفا وما كان من المشركين (الأنعام: 161

Sifa ta farko da take bambance wannan tafarki da sauran tafarkai ita ce riqo da Tauhidi tsagwaronsa, kamar yadda annabawan Allah baki daya suka zo da shi, kuma kamar yadda cikamakin annabawa, Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi. Kuma da yakar shirka da dukkan ressanta, da ‘ya’yanta da nau’o’anta.

Wannan shi ne tafarkin da Allah yake umartar Annabinsa da ya yi shelarsa inda yake cewa:

قل هذه سبيلي أدعوا الي الله على بصيرة أنا ومن اتبعني، وسبحان الله وما أنا من المشركين (يوسف: 108 )

Shi ne tafarkin Annabi (SAW) da wanxada suka bi shi: Sahabbansa da Tabi’ai da Tabi’an Tabi’ai, da wadanda suka bi su da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako. Shi ne tafarkin Ahalus Sunnah wal Jama’a, tafarkin tawagar masu tsira, Alfirqatun Najiya, masu bin dugadugan Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa.

Wani abu mai muhimmanci kuma game da wannan tafarki shi ne gwagwarmaya da sauran tafarkan da suka saba masa: watau tafarkan bidi’a ke nan, kamar tafarkin ‘yan Shi’a Rafilawa da sauransu. Yaqar bidi’a wajibi ne a cikin wannan tafarki namu, domin Allah Madaukaki yana cewa:

وأن هذا صراطي مستقيما فاتبعوه ولا تتبعوا السبل فتفرق بكم عن سبيله (الأنعام: 153 )

Ubangiji, Subhanahu wa Ta’ala, da Ya yi umurni a bi wannan tafarki kuma Ya yi hani ga barin bin wasu tafarkai waxanda za su raba mutane da tafarkinsa.

A tafarkin da muke kira zuwa gare shi, bai isa a yi kira zuwa ga Sunnah kawai, a’a dole kuma sai an yaqi bidi’a. Wannan shi ne abinda duk masu bin wannan tafarki suka yi. Shehu Usmanu Danfodiyo, Allah Ya qara masa yarda, wanda yake shugaba ne shi a wannan tafarki, bai yi IHYAUS SUNNAH ba kawai sai da ya gama da IKHMADUL BID’A. Wannan tsari irin na Mujaddadi Danfodiyo shi ne muke kokarin kamantawa a yau. Kuma aikin fassara wannan littafi, Tafarkin Sunnah, da muke qaddamarwa a yau, da yada shi, ci gaba ne da wancan aiki na Shehu. Wannan wani yunquri ne na sake jaddada tafarkin Sunnah.

Kuma mu sani, ya ‘yan uwa Musulmi, cewa cikin dukkan bidi’o’i na bata, ba’a taba samun mugunyar bidi’a ba kamar bidi’ar ‘yan Shi’a wacce wannan littafi yake mayarwa da martani. A cikin tarihin Musulunci baki xaya, tun daga bullar fitina kawo zuwa yau, ba’a taba yin mugunyar kungiya ba kamar Qungiyar ‘yan Shi’a a wajen akidojinsu da manufofinsu da ra’ayoyinsu da tunane-tunanensu. Ba’a taba yin qungiya mai gaba da zababbun bayin Allah ba irin qungiyear Shi’a. Kungiyar da take gaba da manyan Sahabban Annabi (SAW): Abubakar da Umar da Usman, da sauransu; take nuna qiyayya ga matan Annabi (SAW) Uwayen Muminai: Aisha da Hafsa da wasunsu; kuma ta mayar da la’antarsu a matsayin ibada da take neman kusancin Allah da ita!

Wannan ya sa dukkan malamai mabiya Tafarkin Sunnah suka soke ta kuma suka tsananta gargadi da a guje ta. Sayyidina Hassan binu Ali binu Abi Dalib da qaninsa Sayyidina Hussaini da Sayyidina Ali binu Hussaini, da xaukacin shiyagabanin Ahalul Baiti da malamansu duka sun yi gargaxi a nisance su.

Haka nan manyan malamai kamar su Imam Abu Hanifa da Imam Malik da Imam Shafi’I da Imam Ahmad binu Hambal duka sun tona asirinsu, kuma sun yi gargadi da a guje su. Bukhari da Muslim sun hadu a kan sukar su, da gargadi a nesance su. Shehu Mujaddi Danfodiyo, Allah Ya qara masa yarda, ya soke su mafi kaushin suka, kuma ya yi musu hukunci mafi tsananin hukunci. Ga abinda yake cewa dangane da su: “Wanda duk ya kafirta Sahabbai ko ya ce al’umma ta bata, to shi kafiri ne. Haka nan duk wanda ya yi shakkar kafircinsa, shi ma kafiri ne.” (A duba littafin Tahakikul Isma li Jami’i Dabakati hazihil Ummah na Usman Danfodiyo, shafi na 8).

Saboda haka ya zama wajibi a kan dukkan Musulmi su yaqi akidojin wannan qungiya ta hanyar hikima da wa’azi mai kyau, kamar yadda Allah Ya yi umarni. Ya zama dole a bude wata gagarumar muhawara da ‘yan Shi’a da niyar ceto su daga bata, muhawara ta ruwan sanyi kamar yadda Sheihul Islami Ibnu Taimiya ya yi a cikin wannan littafi da muke qaddamarwa. Wannan kuma har yau, wata sifa ce daga sifofin Tafarkin Sunnah da muke kira zuwa gare shi. Watau tattaunawa ta ruwan sanyi da waxanda aka saba ra’ayi da su, tattaunawa wacce za’a gina ta a kan ilmi ingatacce, ba a kan hayaniya ba da ruxun jahilci.

‘Yan uwa musulmi, a takaice wadannan wasu ne daga cikin sifofin Tafarkin Sunnah wanda muke kira zuwa gare shi. Idan wannan Tafarki ya bayyana ga mutane, to muna kira ga dukkan Musulmi da su tallafawa yunkurin sake jaddada wannan tafarki. Muna ganin wannan aiki wajibi ne a kan dukkan Musulmi saboda waxannan dalilai:

1. Dalili na farko: Wannan tafarki shi ne tafarkin tsira domin shi ne tafarkin Manzon Tsira Annabi Muhammadu (SAW) da Sahabbansa. Ya zo a cikin hadisi, Ma’aiki (SAW) ya ce, ” Banu Isra’ila sun karkasu zuwa qungiya saba’in da biyu, kuma al’ummata za su karkasu zuwa kungiya saba’in da uku; dukkaninsu suna wuta sai guda kawai.” Sahabbai suka ce: Wace ce gudar, ya Ma’aikin Allah? Ya ce, “Wacce nake kai ni da Sahabbaina.” Tafarkin Sunnah da muke kira zuwa gare shi yana koyawa Musulmi su yi riqo da abinda Annabi yake kai da Sahabbansa.

2. Dalili na biyu: Wannan tafarki yana hada kan al’umma wanda kuma shi ne sanadin zaman lafiya a qasa. Tafarkin yana kira ga kowa da ya ajiye ra’ayinsa, a koma gaba daya a yi riqo da abinda Annabi (SAW) yake kai shi da Sahabbansa.

3. Dalili na uku: Riqo da wannan tafarki komawa gida ne da sake gano tushe. Tafarkin Sunnah ba bako ba ne a qasarnan; bidi’a ita ce baquwa. Tunda Allah Ya kawo mana addinin Musulunci a wannan qasa muke bisa Tafarkin Sunnah. Kuma wannan tafarki shi ne abinda shugabanninmu da malamanmu da magabatanmu duka suka tafi a kai. Manyan malamai da aka yi a wannan qasa irin su Muhammad binu AbdulKarim Al-Magili da Shaikh Jibril binu Umar duka sun yi aikin yaxa Sunnah da yaqar bidi’a. Sa’an nan Shehu Mujaddadi ya zo ya shimfixa Sunnah, ya qarfafe ta da qarfin daula kuma ya fatattaki bidi’a.

Babu shakka tarihi yana tabbatar da cewa babban aikin da Shehu ya yi, da shi da almajiransa da mataimakansa da mabiyansa shi ne shinfida Sunnah, da yaxa ta, da koyar da ita ga mutane da kuma aiwatar da ita a rayuwarsu ta yau da kullum. Kuma wannan aiki shi ne abinda zui’arsa suka tafi a kai, kama tun daga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello har ya zuwa yau. Kasancewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi yana zaune tare da mu a yau a wannan taro yana tabbatar da haka. Saboda haka wannan yunquri na sake jaddada Tafarkin Sunnah ba sabon abu ba ne, amma komawa ne ga tushe wanda magabatanmu suka aza mu a kai kuma suka tafi suka bar mu a kai.

Don haka muke kira ga dukkan Muslumi da su goyi bayan wannan yunquri kuma su tallafa masa da duk abinda Allah ya hore masu na ilmi da dukiya da mulki da fadi-a-ji, da sauransu. Muna kira da babbar murya ga Mai Alfarma Amirul Muminina da ya yi amfani da qwarjini da gogewa da fahimtar zamani da Allah Ya ba shi ya jawo hankalin sauran shiyagabanni mataimakansa sarakunan Musulunci na qasar nan duka da su taimakawa wannan yunkuri. Wannan haqqinsu ne, aikinsu ne. Babu shakka wanda duk ke riqe da tutar Shehu to wajibinsa ne ya yi aikin Shehu: Ihya’us Sunnah wa Ikhmadul Bid’a.

Lokaci ya wuce da shiyagabanni za su zama ‘yan kallo a harkar addinin mabiyansu. Yaxuwar bid’a sharri ne ga al’umma. Yana rarraba kawuna kuma ya kawo fitinu. Dan haka lallai shugabanni suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen kaucewa fitinu da rarraba ta hanyar qarfafa guiwar masu kira zuwa Tafarkin Sunnah. Muna roqon mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya isar da wannan kira namu wurin da muryarmu ba ta isa. Ya isar da kiranmu ga Jama’atu Nasril Islam da Majalisar Qoli ta harkokin Addinin Musulunci (SCIA). Kuma ya shawarci masu girma gwamnonin jihohi da su dauki aikin yaxa Tafarkin Sunnah da yakar bidi’a da muhimmanci saboda tabbatar da zaman lafiya da ci gaban talakawansu.

A karshe ina jinjinawa Cibiyar Ahlul Baiti da Sahabbai saboda wannan gagarumin aiki da suka yi na fassara wannan littafi da yaxa shi a tsakanin jama’a. Ina roqon Allah Madaukaki da Ya yi musu sakamakon alheri, Ya qara musu qwazo da basira.

Wassalamu Alaikum.

Dr. Umar Muhammad Labdo